Laraba 4 Nuwamba 2026 - 21:59
Nasarar Gaskiya a Kan Ƙarya Alkawari Ne na Alƙur’ani

Hauza/ Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i, ya bayyana cewa duk wanda har yanzu yake tunanin cewa za a iya sauya halin Amurka ko hana ta ci gaba da gaba da al'ummar Iran ta hanyar sassauta ra'ayi, yana cikin babban kuskure.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza cikin saƙon da ya fitar bisa bikin Ranar Yaƙi da Ƙasashe Masu Girman Kai a Duniya ta Ƙasa,  Jagoran ya bayyana cewa wannan rana tana nuna yadda ɓangaren gaskiya ke fuskantar ɓangaren ƙarya. Ya kuma jaddada cewa al'ummar Iran sun ƙara fahimtar matsayinsu game da Amurka.
Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene'i ya yi bitar tarihin shekaru da dama na gaba da ƙiyayyar da Amurka ta nuna wa al'ummar Iran, inda ya bayyana cewa gwagwarmayar al'ummar Iran da Amurka ba ta takaita ga ranar 13 ga watan Aban kawai ba, domin yanzu kusan kowace rana ta zama ranar tsayin daka da gwagwarmaya.
Ya ƙara da cewa a dukkan matakan da Amurka ta ɗauka, ta ci karo da ƙarfin halin al'ummar Iran da kuma gaskiyar abin da ke faruwa a fagen daga. Ya kuma bayyana cewa hanya ɗaya tilo ta samun cikakkiyar kariya ita ce ci gaba da dabarar gina Iran mai ƙarfi a dukkan fannoni na ci gaba.
Jagoran ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da goyon bayan juna tsakanin al'umma da jami'an gwamnati.
Ga fassarar cikakken saƙon da Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei ya fitar bisa bikin Ranar Yaƙi da Ƙasashe Masu Girman Kai ta Ƙasa:
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.
Yau ita ce Ranar Yaƙi da Ƙasashe Masu Girman Kai a Duniya ta Ƙasa. Rana ce da ta ƙunshi muhimman abubuwan tarihi da suka nuna yadda ɓangaren gaskiya yake fuskantar ɓangaren ƙarya, haka kuma yadda waɗanda ake zalunta suke fuskantar azzalumai.
Wataƙila za a iya cewa a wannan shekara, al'ummar Iran sun fi kowace shekara fahimtar matsayinsu game da Amurka mai aikata laifuka. Amma sake duba tushen wannan ƙiyayya, dalilanta da muhimman abubuwan da suka faru a tarihin gaba da juna tsakanin Amurka da al'ummar Iran, abu ne da zai haska mana hanyar da za mu bi a nan gaba.
Farkon zaluncin Amurka ga al'ummar Iran ya samo asali ne tun sama da shekaru 70 da suka gabata. A lokacin ne Amurka ta shirya juyin mulkin ranar 28 ga watan Murdad domin ci gaba da wawushe arzikin ƙasa da dukiyoyin al'ummar Iran, musamman man fetur.
A shekarun da suka biyo baya, har zuwa nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, mahukuntan Amurka sun yi ƙoƙari matuƙa wajen wawushe dukiyoyin al'ummar Iran.
A wannan hanya, sun taimaka wajen kafa hukumar leƙen asirin SAVAK, tare da samar da yanayin tsauraran matakan tsaro a cikin al'umma. Hakan ya ba azzalumar gwamnati ta wancan lokaci damar murƙushe duk wani yunƙuri na nuna rashin amincewa da manufofinta.
Haka kuma, a gab da nasarar Juyin Juya Halin Musulunci mai girma, Amurka ta yi amfani da dabaru iri-iri domin ganin ta ci gaba da riƙe gwamnatin da take yi wa jagoranci daga waje.
Bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci kuwa, za a iya lissafa ayyukan ƙiyayya da dama da Amurka ta yi wa al'ummar Iran. Daga cikinsu akwai:
* Tallafa wa ƙungiyoyin da ke neman raba ƙasar Iran da masu shirya juyin mulki da kuma munafukai, waɗanda suka kashe manyan masana kimiyya, 'yan siyasa, shugabannin al'umma da kuma dubban fararen hula cikin rashin tausayi.
* Ba wa gwamnatin Ba'ath ta Iraki cikakken goyon baya a lokacin yaƙin da aka tilasta wa Iran a karon farko.
* Kisan fararen hular da ke cikin jirgin saman fasinja.
* Ɗora wa Iran takunkumin tattalin arziki masu yawa da tsanani na tsawon lokaci.
* Shirya da tallafa wa tarzoma da fitintinu daban-daban, har ma da samar da makamai ga waɗanda ke cikinsu.
* Kisan Janar Qasim Sulaimani, gwarzon ƙasar Iran da al'ummar Musulmi.
* Kwace da satar dukiyoyin al'ummar Iran a ƙasashe daban-daban.
* A ƙarshe, kai hare-haren soji kai tsaye a yaƙe-yaƙen da aka tilasta wa Iran a karo na biyu da na uku, inda aka kashe ɗimbin masana kimiyya, kwamandojin soji da kuma al'ummar Iran marasa laifi, tun daga jarirai da ƙananan yara har zuwa tsofaffi. A kan gaba cikin waɗanda aka kashe akwai Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci mai girma, Allah Ya tsarkake ruhinsa.
A duk waɗannan matakai, shugabannin Amurka masu girman kai da masu yi musu biyayya sun kasance suna neman tilasta wa Iran ta shiga ƙarƙashin ikonsu tare da miƙa wuya gare su.
A cikin sabbin matakan wannan danniya, sun cire duk wani abin da suke nunawa na ƙa'idojin ƙasa da ƙasa na ƙarya da yaudara, inda suke bayyana manufarsu a fili ta hanyar neman raba ƙasar, tilastawa al'ummar Iran su durƙusa, rusa tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma lalata tsohuwar wayewar Iran.
Sai dai a duk lokacin da suka ɗauki irin waɗannan matakai, sun ci karo da katangar gaskiyar abin da ke faruwa a fagen daga da kuma ƙarfin azamar al'ummar Iran. Sakamakon kuskuren lissafinsu da tunaninsu na girman kai kuwa, ya kasance asarar kuɗaɗe da manyan matsaloli da suka ɗora wa al'ummar Amurka da gwamnatocin da take goyon baya.
Yanzu labarin tsohuwar ƙiyayyar Amurka ga al'ummar Musulmin Iran da kuma jarumtar al'ummar Iran wajen tsayin daka a gabanta ya kai matakin da ba ranar 13 ga watan Aban kaɗai ba, har ma dukkan ranaku da sa'o'i sun zama lokutan tsayin daka da gwagwarmaya da Babban Shaidan.
A halin yanzu, abin da ke faruwa a Tekun Fasha, musamman mashigar ruwan Hormuz, ya nuna cewa labarin cewa ba za a iya kayar da Amurka ba, ba gaskiya ba ne. Haka kuma, ya bayyana raunin gwamnatocin da suka dogara da ƙasashen waje maimakon dogaro da al'ummarsu, da kuma gazawar manyan ƙasashe wajen kare gwamnatocin da suke goyon baya.
Ɗaukar matakan gudanar da iko da Iran ta yi a mashigar ruwan Hormuz da kuma lalata sansanonin sojin Amurka da ke ƙasashen yankin, duk da cewa martani ne ga zalunci da hare-haren Amurka a yaƙin da aka tilasta wa Iran a karo na uku, amma a lokaci guda ana iya kallonsa a matsayin gwagwarmayar farko ta yankin da ake yi da girman kai na ƙasashen waje. Idan aka sake maimaita irin waɗannan zaluncin, wannan gwagwarmaya za ta iya faɗaɗa fiye da yadda take a yanzu.
Wannan alama ce ta ƙarfin Iran. Haɗe da haɗin kan dukkan sassan ɓangaren gaskiya da kuma ayyukan jarumtaka masu hikima da ƙarfin hali na ƙungiyoyin gwagwarmayar Musulunci, tun daga Falasɗinu da Lebanon zuwa Iraki da Yemen, wannan yana nuna farkon wani sabon yanayi mai cike da fata na ɗaukaka tutar ɓangaren gaskiya da kuma samar da sabon tsarin duniya.
Domin kuwa a duk lokacin da ɓangaren gaskiya ya kasance mai dogaro ga Allah, mai haƙuri da juriya, tare da sadaukar da kai, to ɓangaren ƙarya, ko da yana da ƙarfin soja ko duk wani irin ƙarfi, ba zai iya jurewa a gabansa ba. Ƙarshe, zai ja da baya kuma ya sha kaye. Kamar yadda Allah Ya ce:
إِنَّ الْبَاطِلَ كَانَ زَهُوقًا
"Lallai ƙarya ta kasance mai gushewa ce."
Godiya ta tabbata ga Allah, al'ummar Iran sun koyi manyan darussa daga koyarwar Musulunci na Annabi Muhammad (S.A.W.W.), da kuma koyarwar Juyin Juya Halin Musulunci da makarantar shugabanninsu masu hikima, Imam Khumaini da Shahidin Jagora Imam Khamene'i, Allah Ya ɗaukaka matsayinsu.
A sakamakon haka, kullum imaninsu yana ƙara zurfafa game da gaskiyar wannan hanya, musamman ganin yadda alƙawuran Allah suke ci gaba da bayyana a zahiri.
A yau, sakamakon kunyar da masu girman kai suka jawo wa kansu, ƙarfin Amurka da ikonta suna ci gaba da raguwa ta fuskar ƙarfin soja da kuma tasirinta a duniya. Wannan koma baya ya kai matakin da ba za a iya dawo da shi ba, kuma rushewar ikonta tana ƙara sauri.
Idan har yanzu akwai waɗanda suke da ɗan ƙaramin fata cewa Amurka za ta sauya halinta, ko kuma sauyin jam'iyya da shugabanni a tsarin mulkinta zai sauya manufofinta, ko kuma suke tunanin cewa za su iya hana ta gaba da al'ummar Iran ta hanyar ba ta rangwame ko sassauta ra'ayi, to suna cikin babban kuskure.
Irin wannan tunani na ƙarya tamkar rashin godiya ne ga manyan nasarorin da al'ummar Musulmin Iran suka samu ta hanyar dogaro ga Allah, haƙuri, juriya da gwagwarmaya.
Babbar manufar Babban Shaidan ita ce ganin al'ummar Iran sun miƙa wuya gare shi ba tare da wani sharaɗi ba. Saboda haka, duk wani ɗan yunƙuri na karkata zuwa ga miƙa wuya ga maƙiyi mai neman mamaya zai iya jefa manyan nasarorin da aka samu ta albarkacin jinin shahidai da sadaukarwar al'umma cikin haɗari. Haka kuma, hakan zai ƙara wa maƙiyi ƙarfin guiwar ƙara buƙatu da kuma sake kai hare-hare da aikata wasu laifuka a nan gaba.
Hanya ɗaya tilo ta kaiwa ga cikakkiyar kariya ita ce ci gaba da dabarar gina Iran mai ƙarfi a kowane fanni, tare da ci gaba da samun nasara a dukkan fannoni na ci gaba.
Haɗin kai, haɗuwar zukata da kuma zaman tare cikin fahimtar juna a tsakanin al'umma su ne muhimman ginshiƙan samun nasara a wannan hanya. Wajibi ne waɗannan abubuwa su zama tushen dukkan maganganu da ayyukan al'umma da jami'an gwamnati.
A wannan fanni, kamar yadda goyon bayan al'umma ga jami'an gwamnati yake da muhimmanci, haka ma wajibi ne jami'an gwamnati su ci gaba da ƙara himma wajen yi wa al'umma hidima cikin gaskiya da ƙwazo, kusanci da jama'a, samar da abubuwan more rayuwa da inganta tattalin arziƙinsu, da kuma tabbatar da ci gaban rayuwarsu ta zahiri da ta ruhaniya, tare da kare mutuncinsu da 'yancin kansu.
Matasa, ɗaliban jami'o'i da kuma ɗaliban makarantu su ne ginshiƙan farko wajen gina kyakkyawar makoma mai ɗaukaka ga ƙasarmu Iran.
Wajibi ne su ci gaba da fafutukar rushe gidan duhun yanke ƙauna, rashin fata da tunanin cewa ba za a iya cimma wani abu ba, tare da buɗe ƙofar hasken fata da tunanin cewa za mu iya cimma nasara.
Domin gudanar da wannan aiki, wajibi ne matasa su kasance masu shiri sosai, su kuma tanadi makaman ilimi, tsoron Allah, ƙwarewa, kyawawan ɗabi'u, azama da ƙoƙari na musamman. Haka kuma, wajibi ne su yi alƙawarin haɗin kai da juna domin cimma manyan manufofi.
Ina fatan da taimakon Allah da addu'ar Jagoranmu Imam Mahdi (A.F), al'ummar Iran za su samu nasara, farin ciki da ci gaba a dukkan fannoni cikin gaggawa, sannan a samar da yanayin da zai taimaka wajen ƙara rugujewar ikon Babban Shaidan cikin sauri.
إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُ بَعِيدًا وَنَرَاهُ قَرِيبًا
"Lallai su suna ganin hakan abu ne mai nisa, amma mu muna ganin sa yana kusa."
Sayyid Mujtaba Husaini Khamene'i 
13 ga watan Aban, 1405 (4 ga Nuwamba, 2026).

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha